Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta cafke wani haramtaccen mai fataucin miyagun kwayoyi, Kabiru Mahmud dan shekara 21 a Danbare dake karamar hukumar Kumbotso, tare da wasu buhhunan busassun ganyan tabar wiwi 49.
Daya ke tabbatar da kamun matashin Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da cafke Mai laifin ga manema labarai a Kano ranar Laraba.
Ya bayyana cewa a ranar 24 ga watan Nuwamban shekara 2020, jami’an ‘yan sanda na Puff adder yayin da suka kai samame maboyar masu aikata laifi a yankin Danbare, sun kama wanda ake zargin tare da kayayyakin da ake zargin tabar wiwi ne.
A lokacin da rundunar ‘yan sandan ke bincikar Matashin ya fallasa cewa, Tabar wiwin mallakar mahaifin sane wanda yakasance Dilanta ne.