fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Yadda jami’an tsaro suka yi artabu da barayin daji a yankunan Zamfara:An kashe da dama

Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta murkushe yunƙurin da wasu ‘yan fashin daji suka yi na sace wani mutum da iyalinsa a ƙarshen mako.

Shaidu sun fada wa BBC cewa maharan sun shiga unguwar Mareri da ke Gusau babban birnin jihar da daddare inda aka yi musayar wuta.

Sai dai jami’an tsaro sun yi musu kwanton-ɓauna kana suka kuɓutar da wadanda suka yi garkuwa da su.

A yankin Bukuyum m, jami’an tsaron ne suka yi galaba a kan ‘yan fashin dajin inda shaidu suka bayyana cewa an kashe da dama daga cikinsu.

‘Yan fashin dajin dai sun kwashi kashinsu a hannu, yayin da sojoji da sauran jami’an tsaro suka yiwa musu kwantan ɓauna a unguwar ta Mareri da ke birnin Gusau na jihar Zamfara.

Wani makwabcin mutumin da ‘yan bindigar suka yi kokarin sace shi da iyalinsa, ya ce, an yi ta harbe-harbe babu kakkautawa tsakaninsu da jami’an tsaro cikin dare, kuma Allah ya bai wa jami’an tsaron nasara a kan barayin dajin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya shaida wa BBC cewa an sanar da su aukuwar lamarin, sai suka aika da jami’ansu inda suka hana ‘yan bindigar tafiya da mutanen da suka sata.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun fafaro mazauna kauyukan inda suka far musu tare da sace dukiya, ya ce an yi bata-kashi tsakanin ‘yan bindiga da jami’an tsaron an kuma kashe ɓarayin dajin da dama.

Kazalika mutumin ya ce daga abin da ya gani babu wanda ya jikkata daga ɓangaren sojojin.

Kawo yanzu dai sojojin Najeriya ba su yi karin haske ba game da artabun da suka yi da ‘yan fashin dajin.

‘Yan fashin daji na ci gaba da kai munanan hare-hare a ciki da wajen jihar Zamfara, inda lamarin kan kai ga rasa rayuka da dumbin dukiya da awon gaba da wasu mutane.

Sai dai ana su ɓangaren jami’na tsaro da gwamnatin jihar har da Tarayya na cewa su na bakin kokarinsu domin shawo kan wannan matsala.

Ko a baya-bayan nan sai da gwamnatin Najeriya ta kaddamar da gagrumin aikin kakkabe ‘yan bindigar da ke kai hare-hare a wasu yankunan jihar Neja.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.