fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Yadda mai ba da hannu a titi ta zama Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Najeriya

Mai Shari’a Bolna’an Monica Dongban-Mensem, mai bayar da hannu a titunan babban birnin Najeriya Abuja (bisa radin kai) ce ta zama Shugabar Kotun Daukaka Kara a Najeriya.

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Mai Shari’a Monica a mukamin na rikon kwarya ne biyo bayan ritaya da Zainab Bulkachuwa ta yi.

 

Zainab Bulkachuwa ta shafe shekara 43 a harkokin shari’a, sannan ta shafe shekara shida a matayin shugabar kotun daukaka kara.

 

Wannan nadi yasa Justice Monica ta zama mace ta biyu da ta shugabanci Kotun Daukaka kara ta Najeriya.

 

A lokacin da ba ta aiki, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem kan je titi ta rika bayar da hannu a Abuja.

 

Monica Dongban-Mensem ‘yar asalin Jihar Filato ce, kuma ita ce Shugabar Kotun Daukaka Kara reshen Jihar Inugu kafin yanzu.

 

Ta yi karatun digirinta na farko da na biyu a bangaren shari’a a Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.

 

 

A lokacin da ba ta aikin komai, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem kan je titi ta rika bayar da hannu a Abuja, shekara takwas bayan da wani ya kade danta da mota, ya mutu.

 

Idan ka gan ta za ka tabbatar lallai aikin ta fito yi da gaske, kamar yadda wakiliyar BBC ta sashen Pidgin ta ruwaito kwanakin baya da ta ci karo da ita tana kan aikin nata.

Karanta wannan  Bideyo: Kalli rawar da gwamna Wike yayi yayin dayake kaddamar da babbar hanyar daya yi a jihar Patakwal

 

“Mafi yawancin ‘yan Najeriya dai ba su da hakuri, kuma ana iya gani ma ko a tukinsu,” in ji Monica.

 

‘Yar kimanin shekara 62, Monica ta kafa wata kungiya da ta sanya wa sunan danta – Kwapda’as Road Safety Demand.

 

Ta yi hakan ne domin a rika horar da masu tuka mota a kan yadda za su rinka kiyayewa, sannan kuma tana shirin samar da makarantar koyon tuki ga direbobin motocin haya.

 

Ba a nan kawai ta tsaya ba, Justice Dongban-Mensem, na son ta rinka bayar da hannu da kanta.

 

Bayan ta shafe wasu makonni tana karbar horo a hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Najeriya, ta samu shaidar cewa za ta iya bayar da hannu a tituna.

 

A lokacin, shekara biyar da mutuwar danta, anan ta ziyarci wajen da aka kade danta a tsakiyar birnin Jos na jihar Filato.

Rahoton BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.