Saturday, July 20
Shadow

Yadda mai ciki zata kwanta

Masana sun yi amannar cewa, da zaran ciki ya fara girma, an fi son mace ta kwanta a bangaren jikinta na hagu tare da lankwasa gwiwowin kafarta.

Wannan tsarin kwanciya a cewarsu shine mafi jin dadi sannan zai taimakawa gudanar jini a jikin uwar da danta.

Hakanan a cewar masanan, wannan salon kwanciyar yana hana kumburar kafar me ciki.

Masana kiwon lafiya sunce kwanciyar ruf da ciki bata da illa idan ciki be girma ba amma idan ya girma a daina yinta.

Masana sun ce kwanciya a gefen dama yana da illa amma kuma me ciki zata iya kwanciya a gefen dama na dan gajeren lokaci.

Hakanan masana sun yi gargadin kada a kwanta rigingine, watau akan baya musamman idan ciki yayi nisa.

Karanta Wannan  Gwajin ciki da sugar

Kwanciya akan baya na hana jini gudana yanda ya kamata a jikin me ciki da kuma dan dake cikinta.

Hakanan kwanciya akan baya zata iya haifar da ciwon kwankwaso, wanda mafi yawan mata masu ciki na fama dashi.

Hakanan kwanciya akan baya yana sa mace ta rika munshari da fuskantar sauran matsalolin numfashi.

Daga sanda ciki ya kai sati 20, ba’a son mace ta kwanta akan gadon bayanta.

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *