fbpx
Monday, August 15
Shadow

Yadda ruwan sama ya kashe wata mata ya tafi da gidaje 70 a jihar Kano

Wata mata ta rasa ranta yayin da mutane da dama suka samu raunika sakamakon ruwan sama mai karfin gaske da aka yi a jihar Kano.

Wannan lamarin ya faru na a Anguwar Bai da kuma Dukawa dake karamar hukuma Danbatta, kuma hukumar dake bayar da agajin gaggawa ta ziyarce su.

Inda shugabanta Dr. Saleh Jili ya mika sakon ta’aziyyar ga iyalan matar data rasa ranta kuma ya basu tallafi tare da sauran mutanen da wannan iftila’in ya shafa.

Saleh ya kara da cewa gwamnatin jihar Kano na cigaba iya bakin kokarinta don ganin cewa ta rayukan al’ummarta a fadin jihar bakidaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.