Yaran wani mutun dn shekara 70 Cletus Ofem, Esther da Aaliyah sun bayyana cewa sojoji sun babbake mahaifinsu tare da gidansu baki daya.
Yaran sun bayyana cewa al’ummar karamar hukumar Yukurr dake jihar Patakwal ne sukayi fada da sojojin har suka kashe daya daga cikinsu.
Saboda haka ne sojojin suka dawo daukar fansa wanda anan ne suka babbake masu mahaifin nasu.
Inda yaran suka kara da cewa mahaifin nasu ba zai iya tserewa ba yayin da sojojin sukaje gidan domin bashi da lafiya sosai, kuma sojojin sun san cewa mahaifin nasu yana cikin gidan.