fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Yadda Suka Kashe Hanifa Duk Da An Biya Su Kudin Fansa Naira Milyan Biyar

Yadda Suka Kashe Hanifa Duk Da An Biya Su Kudin Fansa Naira Milyan Biyar

Jami’an ‘yan sanda sun damke mai wata makaranta mai zaman kanta mai suna Noble Kids School da laifin sace wata dalibar sa mai suna Hanifa Abubakar ‘yar shekara 5 tare da kashe ta.

Majiyoyin iyalan yarinyar sun ce yana daga cikin mutanen farko da suka zo jajanta wa iyayenta bayan sace ta, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

“Ya cika da kuka a lokacin da ya ziyarci iyalan domin ta’aziyyar sace yarinyar,” in ji kawun yarinyar, inji Kawun yarinyar mai suna Suraj Sulaiman.

Karanta wannan  Shugabar Kungiyar Taimakon Yara Da Mata Mabukata Ta Kasa Ta Rasu Sakamakon Mummunan Hadari

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar a ranar Alhamis ta ce malamin makarantar, Abdulmalik Tanko ne ya sace ta.

Daga Haji Shehu

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.