fbpx
Saturday, August 13
Shadow

Yadda wani gwarzon direba ya tsiratar da fasinjojinsa 18 bayan ‘yan bindiga sun bude masu wuta a jeji

Wani gwarzon direba dan jihar Patakwal ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka bude masa wuta a hanyar Abonema-Degema-Emuoha.

Inda yace ‘yan bindigar sun so kashe shi ne domin su dauki motar tasa kuma suyi garkuwa da fasinjojin nasa.

Amma cikin ikon Allah Godwin ya tsiratar dasu amma shi ya samu raunika sakamakon harbinsa da ‘yan bindigar suka yi.

Ya kara da cewa abinda ya bashi mamakai shine cikin fasinjonin babu wanda ya damu da yanayin da yake ciki, kawai ce masa suka yi yayi hakuri suka kara gaba abinsu, ‘yan uwansa durebobin Union ne suka kai shi asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published.