Wani insfeto a jihar Nasarawa ya yiwa ‘yar ‘dan ‘uwansa fyade wacce ke zaunne a hannunsa ‘yar shekara 15 wanda hakan yasa ta samu ciki.
Lauyar dake aiki a ma’aikatar lauyoyin mata, Mrs Rabi’atu Addra ce ta bayyana hakan a babban birnin jihar Nasarawan, wato Lafia ranar laraba.
Daily Trust ne suka ruwaito labarin kuma lauyar ta kara da cewa zata yi iya bakin kokarinta don ganin cewa an hukunta shi kuma mutane sun dauki darassi.