Wani magidanci a yankin Lekki Phase 1 dake jihar Legas ya babbaka gida sa saboda ya samu sabani da matar sa.
wannan lamarin ya faru ne a ranar lahadi kuma shugaban hukumar hukumar dake kashe wuta, Adukunke Hassan ya tabbatar da faruwar shi.
Inda yace wani mutun ne ya sanar dasu mai suna Kola, kuma sun hanzarta zuwa gidan sun kashe wutar domin kar ta shafi sauran gidajen dake kusa dasu.
Kuma a yadda ya fahimci lamarin magidanci ya samu sabani da matarsa ne shekaru biyu da suka gabata wanda hakan yasa ya koma wani gidan nasa da zama.
Magidancin wanda ya kasa fadin sunansa kwatsam ranar lahadi yazo da fetur ya babbaka gidan tare da matarsa da yaransa a ciki.