Rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun sun yi nasarar damke wani dan shekara 54, Dauda Bello bayan ya kashe wata mata Mrs. Mesesi Adisa kuma ya sayar da wasu sassan jikinta.
Mai magana da yawun hukumar, Abimbola Oyeyemi ne ya tabbatar da wannan labarin inda yace sun kama shi ne bayan da suka tsananta bincike akan batan matar.
Kuma yace masu tare da marigariyar suke aikin safarar yaran mutane kafin ya kashe ta ya cire wasu sassan jikin nata ya binne ta a daji.
Ya kashe tane saboda yana tunanin kamar tanada wasu makudan kudi a jikinta yayin da suke shirya harkallarsu, amma sai yaga 22,200 ne a jikinta saboda haka ne ya cire wasu sassan jikinga ya binneta amma hukuma ta hakota.