fbpx
Monday, August 15
Shadow

Yadda wani matashi a jihar Kano ya kusa kashe kansa saboda shugaba Buhari yaki yin murabus

Wani matashi dan shekara 25, Hamza Yahaya yayi kokarin kashe kansa a jihar Kano saboda shugaban kasa Muhammdu Buhari yaki yin murabus.

Hamza Yahaya ya hau kan gadar dake kofar Nasarawa ne a jihar Kano ranar juma’a yana kokarin fadowa wanda hakan ya jawo hankulan al’umma sosai.

Inda wani bawan Allah, Abduahi Madugu ya bayyanawa manema labarai cewa shi yana kan hanyar zuwa masallacin juma’a ne sai yaga mutane sun taru wanda hakan yasa shima ya jinkirta.

Kuma yace ba zai wuce wannan matashin yayi hakan bane don halin da Najeriya ke ciki a yanzu ba, amma daga bisani hukumar dake kashe gobara ta hanzarta zuwa ra ceto rayuwar matashin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.