fbpx
Monday, August 15
Shadow

Yadda wani matashi dan shekara 25 ya fada rijiya ya mutu a jihar Kwara

Wani matashi dan shekara 25 ya fada rijiya a Omo Aran dake karamar hukumar Iropodun a jihar Kwara ranar litinin.

Banji Adebayo ya mutu a ciki rijiyar ne bayan ya fada cikinta.

Kuma mutanen dake cikin gidan na Ile Nla sun bayyana cewa yaje dibar ruwa ne a cikin rijiyar sai kafar shi ta zame ya fada ciki ya mutu.

Hukumar dake kashe wuta sun tabbatar da faruwar wannan lamarin, inda mai magana da yawunta Hassan yace sun ciro shi a rijiyar kuma sun mikawa ‘yan uwansa a gaban hukuma.

Leave a Reply

Your email address will not be published.