fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Yadda wani uba ya yi wa ƴarsa mai shekara 3 fyaɗe a jihar Bauchi

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi, ta ce ta kama wani uba da ake zargi da yi wa ƴarsa mai shekara 3 fyaɗe a Unguwar Doya, da ke ƙaramar hukumar Kirfi a jihar Bauchi.

Wata sanarwar rundunar ta ce mahaifiyar yarinyar ce ta kai ƙorafi ofishin ƴan sandan yanki, inda ta shaida musu cewa ”Mijina Ali Lawan ya buƙaci in kai masa tabarma don ya kwantar da ita ta yi barci a ranar 9 ga watan nan”.

”Ina komawa ɗakin na tarar da ita magashiyyan tana ta gumi sharaf-sharaf da amai, sannan gabanta ya kumbura yana zubar da jini” in ji mahaifiyarta.

Bayan ta sanar da ƴan sandan ne aka tura jami’ai cikin shiri, waɗanda su kuma suka kai ta babban asibitin ƙaramar hukumar ta Kirfi don samun kulawa.

Daga baya dai binciken likitoci ya tabbatar da cewa fyaɗe aka yi wa wannan yarinya da muka zaɓi mu sakaye sunanta.

Sanarwar ƴan sandan ta ce an kama mahaifin na ta, kana ana ci gaba da bincike kafin gurfanar da shi a gaban kotu.

Lamarin ya faru ne a garin Faggo da ke ƙaramar hukumar Shira a jihar ta Bauchi.

Ɗan majalisar da ke wakiltar yankin Honarabul Bello Muazu Shira, wanda ya tayar da batun a majalisar dokokin jihar ya yi kiran a gaggauta kama mutumin kan zargin yi wa ƴar shekara bakwai fyaɗe.

“Ya yi wa yarinyar barazana da makami ya yi mata fyaɗe,” in ji shi

A baya-bayan nan gwamnatin jihar ta Bauchi ta kafa wata doka da ta kira VAPP wadda a turance ake kira Violence Against Persons Prohibition, ta kuma tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da laifin yi wa yara kanana Fyaɗe.

Haka ma dokar ta tanadi ɗaurin rai da rai ga wanda ya yi wa babbar mace fyaɗe, da kuma ɗaurin shekaru 20 ga waɗanda suka yi wa mace daya taron dangi.

Hukumomin ƴan sanda a jihar sun ce sun sha samun rahotannin aikata fyaɗe a jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.