fbpx
Friday, February 26
Shadow

Yadda Wasu Matan Najeriya Suka Gayyaci Wani Ba’indiye Domin Yi Masa Tausa, Suka Yi Masa Fashi Kudin $ 70,000 – ‘Yan Sandan Dubai

Wani gungun mata hudu sun yi wa wani Ba’indiya mai shekaru 33 da haihuwa fashi kudi Rs 55,30,806 bayan an yaudare shi zuwa wani wurin yin tausa na bogi ta hanyar manhajar neman aure, kamar yadda wata kafar yada labarai ta ruwaito.

An saurari karar a Kotun ta Farko, kamar yadda jaridar Gulf News ta ruwaito.

A cewar bayanan kotu, wanda aka abun ya shafa, ya ga ana talla wajen yin tausa Akan kudi Dirham 200 (Rs 3,950) tare da hotunan kyawawan ‘yan mata a cikin hotunan tallar.

Sai ya tuntubi lambar da aka bayar akan tallar sannan ya tafi wani gida a yankin Al Refaa na Dubai a watan Nuwamba na 2020.

Hakama an, yana shiga gida sai ya ga wasu mata ‘yan Afirka hudu a cikin gidan, sai suka ce ya bude takardar bankin nai [a wayar salula] ya tura masu kudi.

Sun yi masa barazana da wuka a maqogwaronsa kuma sun mare shi a fuska.

Daya daga cikin matan sai ta dauki katinsa ta cire Dirham 30,000 (Rs 5,92,586) daga ATM.

An kuma ce, sun tsare shi a cikin gida na kwana daya yayin da matan suka kwashe Dirhami 250,000 (Rs 49,38,219) daga asusunsa.

A cewar ‘yan sandan Dubai, an kame wasu mata‘ yan Najeriya uku daga Sharjah bayan an gudanar da bincike mai karfi, yayin da mace ta hudun har yanzu ba ta ji ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *