fbpx
Friday, August 12
Shadow

Yadda wata malamar jami’ar jihar Uyo ta fara sayar da dankali saboda yajin aikin ASUU

Wata malamar jami’ar dake jihar Akwa Ibom a Uyo, Christiana Pam ta fara sayar da dankali domin ta cigaba da daukar dawainiyar kanta saboda yajin aikin ASUU.

Malamar ta bayyana cewa shekara daya kacal tayi tana koyarwa a jami’ar kafin su fara yajin aikin a watan febrairu daya gabata.

Kuma a farko tasha gwamnatin tarayyar zata biya masu bukatunsu su koma aiki ne amma sai taga gwamnatin tarayyar ta share su.

Wanda hakan yasa ta nemi sana’ar hannu domin ta cigaba da daukar dawainiyar kanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.