by hutudole
Wata ma’aikaciyar gwamnati a Babban Asibitin Gwamna Awan a jihar Kaduna, Misis Hannatu Tanko ta bayyana cewa ta yi amai da jini bayan ta karbi allurar rigakafin ta COVID-19.
Misis Tanko ta ce ta sha allurar ne a ranar 25 ga Maris din 2021 kuma daga baya ta ji jiri.
Ta bayyana cewa a ranar asabar 28 ga Maris ta fara aman jini sai aka garzaya da ita asibiti.
Tanko a wani bidiyo mai dauke da hoto ta ce anyi mata allurar ne a sakatariyar Kaduna ta Kudu saboda an fada musu cewa idan basuyi ba, ba za a biya su albashi ba.
“Ina ta yin amai da jini ta hanci da baki. An kai ni asibitin Gwamna Awan, inda aka ba ni magunguna don rage ciwo.
”Sun yi min allura don rage min ciwon kai sannan suka ce in zo a gwada ni. Ni kuma an ce in sayi panadol. Na bar asibitin ne saboda ba sa yi min komai.
Misis Tanko wacce yanzu haka take karbar magani a Asibitin Kwararru na Ashmed da ke Trikania, Jihar Kaduna ta ce tana samun sauki saboda sun yi mata allura mai yawa don rage mata radadin.
Lokacin da aka tambaye ta yi wannan allurar ne don radin kanta sai ta ce, “An gaya mana a wurin aikinmu cewa idan ba mu dauki allurar ba, ba za a biya mu ba. Tunda ni nake ciyar da iyalina kuma mahaifiyata ba ta da lafiya, sai na sha allurar domin a biya ni. ”