fbpx
Monday, December 5
Shadow

Yadda ‘yan bindiga suka kashe mahaifina – Dan Shugaban APC na jihar Osun

Aregbesola, dan shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Atakumosa ta Gabas ta jihar Osun, Cif Gbenga Ogbara, ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka kashe mahaifinsa.

Aregbesola, wanda ya samu raunin harsashi yayin harin tare da mahaifiyarsa, Ruth, ya yi magana da jaridar The Nation ranar Litinin a kan gadon asibiti.

A cewarsa: “Muna fitowa daga shagon jiya tare da mahaifiyata, sai muka ga wasu mutane a kan babur.

“Bayan mintuna kaɗan, ɗaya daga cikinsu ya buga gate ɗinmu yana neman ya ga mahaifina. Da ya matso kusa da kofar zai bude, sai mahaifina ya fahimci abunda suka zo yi kuma ya yi yunkurin guduwa amma suka harbe shi a baya sau da yawa.

“Maharan sun harbe mu ta taga kuma daya daga cikin harsashin ya same ni a hannuna na hagu.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *