fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Yadda ‘yan bindiga suka sa makarantun gwamnati suka tursasa dalibai suka rubuta jarabawa 13 a rana guda

Wasu makarantun sakandiri a babban birnin tarayya Abuja sun tursasa dalibansu sun rubuta jarabawa har guda 13 a rana guda.

Wannan lamarin ya faru ne biyo bayan wasikar da ‘yan bindiga suka turawa makarantun cewa zasu kawo masu hari bada dadewa ba.

Wanda hakan yasa ma’aikatar ilimi ta umurci a kulle gabadaya makarantun gwamnatin dake fadin jihar biyo bayan wasikar ‘yan bindigar.

Dalibai da dama sun koka kan wannan jarabawar da suka rubuta inda sukace sunje makaranta ranar talata ne da niyyar rubuta jaraba daya zuwa biyu, amma aka tursasa su suka rubuta har 13.

Leave a Reply

Your email address will not be published.