‘Yan bindiga sun yanke hannun wani jariri dan watanni biyar a duniya yayin da kuma suka kashe mutane takwas hadda yara hudu a jihar Filato.
‘Yan bindigar sun kai wannan harin ne a ranar lahadi 31 ga watan Yuli da misalin karfe 10 na dare a Kauyen Danda dake kudancin jihar Filato.
Kuma duk ‘yan uwa ne suka kashe a hari da suka kai, yayin da kuma wani ji jinjiri da suka raunata ya rasu ranar litinin a asibiti.
Sanatan dake wakiltar yankin da wannan abin ya faru, Bagos ya rattaba hannu akan takaddun tsige shugaba Buhari don yace abin ya fara gona da iri.