fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Yadda ‘yar shekara 80 ta zagaye kasashen Afirka a mota

South Africa Map
A yayin da mutum ya kai shekara 80 a duniya, wani zai yi tunanin lokaci ya yi ya daina wasu abubuwa, sai dai batun ba haka yake ba ga wata dattijuwa Julia Albu ‘yar kasar Afirka ta Kudu.
Don kuwa a ranar da ta cika shekara 80 a duniya ne ta dauki ‘yar tsohuwar motarta domin fara rangadi a nahiyar Afrika.

Haka zalika ta dauki tanti da tukwane da kuma kayan sawa ne kafin ta dauki hanya a watan Yunin da ya gabata.
Sai dai ta dawo Afirka ta Kudu inda take jiran bizarta ta zuwa Sudan kafin ta kara daukar hanya.
Dattijuwar dai na rubuta bayanan abubuwan da ke faruwa a yayin wannan rangadi da suka hada da gudunmawar da ake bayarwa na wani shirin tallafi da take kira SHINE, wanda ake koyar da yara karatu.
Wakilin BBC Mohammed Ali ya tambaye ta shin ko lokacin da za ta fara rangadin an yi kokarin hana ta?
“Kowa, kowa ma cewa yake ba zan iya ba. Hakazalika wasu ma sun ce mini za ki iya, kuma za ki yi tafiyar ko suna so ko basa so. Kuma nima ko ina so ko a’a,” in ji ta.
Ganin shekarunki 80, daukar doguwar hanya, haka tuki zai yi miki wahala, ya kike yi?
“Za ka samu wani ne ya tuka ka, kuma abin da ‘ya’ya na ke yi ke nan sun kyauta mini, ‘ya’ya na mata sun kyautata sosai, dana ya zo daga Austarlia.”
Ta ci gaba da cewa: “Surukina zai zo kuma yanzu na samu wanda zai dauki nauyi na. Ya yi min tayin ya tuka ni zuwa wani bangare na tafiya ta. Ni ma ina tukin, sai dai na fi son na dauki hotuna ne a tsawon tafiyar.”
Har ila yau dattijuwar ta ce: “Idan muna tafiya ina so in tsaya don in dauki hoto ko kuma na yi magana da wani. Akwai wani da muka hadu da shi yana dauke da wata doguwar sanda da baraye masu yawa a kyafe.”
“Yayi mini tayi sai na ce masa idan ba zaka damu ba, a’a,” in ji ta.
Da aka tambaye ta wadanne abubuwa ne suka fi daukar hankalinki, ta ce:
“Suna da dama kam, abin dai da ya fi jan hankalina shi ne lokacin da muka isa wani rami dake tsaunin gongora. sai muka yi tafiya na tsawon sa’a uku da rabi zuwa wajen Surengeti.”
Ta ci gaba da cewa: “A wannan karshen makon da muka isa suna wani biki na ‘yan kabilar Masai kuma akwai mayaka 69 suna sanye da kayayyaki masu kayatarwa, da duwatsu na ado. Suna ta tsalle-tsalle kala-kala. Abin da ya fi daukar hankalina ke nan.”
Yayin da take kan hanyar komawa Nairobi, inda za ta dauki motarta ta ci gaba da tafiya, an tambayeta kamar tsawon wanne lokaci take tsammani zai dauke ta ta kammala rangadin?
Sai Julia ta ce tana ganin zai dauke ta wata uku har ta isa birnin Addis Ababa.
Ta ce: “A can kuwa saboda na hadu da mutane da dama ta shafukan sada zumunta na Facebook da shafin da nake rubutu na intanet.”
“Duk sun gayyace ni na sauka a wurinsu, sun kuma shirya kaini naga mujami’u. Kuma ka san sun ce Malawi ita ce ruhin Afrika, Uganda kuma Lu’luun Afrika.”
Dattijuwar ta ce za ta zuwa inda ake wa kirari da taskar zinariyar Afrika, don ta ce akwai abubuwan ban sha’awa sosai can.
“Wasu na cewa saura mako uku ya rage mini a’a zan yi tafiya har tsawon lokacin da ya kama. Sannan zan je Sudan, don ace mutanen kasar suna da kirki sosai kuma akwai abubuwan bude ido sosai.”
“Sannan zan nufi Masar kasar da nake kaunar zuwa, hakan zai kai ni tsakiyar watan Janairu kafin na kammala duk wannan,” in ji ta.
bbchausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  An saka dokar hana fitar dare a jihar Anambra

Leave a Reply

Your email address will not be published.