A yayin da shugaban kasa da majalisar iyayen kasa suka yafewa tsaffin gwamnonin Filato da Taraba, Watau Joshua Dariye da Jolly Nyame satar kudin talakawa da suka yi, ‘yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyi akan lamarin.
Ranar Alhamis data gabata ne dai shugaban kasar da majalisar iyayen kasan suka yi wannan yafiya wadadda ta hada da karin wasu mutane 157.
Ciki kuwa hadda wani janar din soja da ya fito daga dangin su tsohon shahararren mawakin Najeriya, Fela, wanda aka daureshi saboda nuna tsoro wajan yaki da Boko Haram.
Lauyoyi da kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun bayyana cewa hakan bai dace ba.
Domin zai karfafa ‘yan siyasa su ci gaba da satar dukiyar Talakawa ido rufe.
Koda a jiya dai, saida gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya bayyana cewa wannan mataki, ya nuna ikirarin yaki da rashawa da cin hanci na gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba da gaske bane.