Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya caccaki gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan yafewa gwamnonin Taraba da Filato laifin almundanar da suka yi.
Wike yace hakan ya sabawa ikirarin gwamnatin shugaban kasar na yaki da rashawa da cin hanci.
Wike ya bayyana hakane a Minna bayan ganawa da wakilan jam’iyyar PDP a kokarinsa na neman kuri’arsu kamin zaben fidda gwani.
Wike yace wannan yafiya ta wofintar da kokarin kotu da ta yi na shafe shekaru ana shari’a kamin daure gwanonin da kuma kokarin hukumar yaki da rashawa ta EFCC.