fbpx
Monday, August 15
Shadow

Yajin aikin ASUU: Bulaliyar majalissar dattawa ya fadawa shugaba Buhari ya daina yin wasa da ilimin matasan Najeriya

Bulaliyar majalissar dattawa, Orji Kalu yahi kira ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari cewa su daina wasa da ilimin matasan kasar.

Orji Kalu ya bayyana hakan ne a yau ranar alhamis inda yace bai kamata gwamnatin ta zuba ido tana ganin kungiyar malamai ta ASUU na cigaba da yajin aiki na tsawon watanni ba.

Inda yace ya kamata gwamnatin tarayya ta gaggauta kiran kungiyar malaman domin ta biya masu bukatunsu yara su koma makaranta.

Kungiyar malaman ta fara yajin aiki ne tun a watan febrairu wanda hakan yasa suka kulle gabadata jami’o’in kasar kuma har yanzu gwamnati bata biya masu bukatunsu sun koma aiki ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.