fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Yajin aikin ASUU: Gwamnatin Buhari batasan darajar ilimin Najeriya ba, cewar Sanusi Lamido

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya na CBN Sanusi Lamido Sanusi ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari kan yajin aikin da kungiyar makamai ta ASUU keyi.

Kungiyar malaman ta kasance tana yajin aiki na tsawon watanni bakwai tun a watan febrairu na wannan shekarar kuma gwamnatin tarayya bata biya masu bukatunsu ba.

Wanda hakan yasa tsohon Gwamnan CBN din ya caccaki gwamnatin Buhari yace bata san darajar ilimnin Najeriya sai yasa ta bar ASUU tana wannan yajin aikin.

Ya kara da cewa malamai ba karamin sadaukarwa sukeyi ba wurin ilimintar da yara, dominsuna da nasu burin amma suka zabi ilimintar da yara domin  taimakawa kasa saboda haka ya kamata a riga kyautata masu.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.