fbpx
Monday, August 15
Shadow

Yajin Aikin ASUU: Ministan Ilimi ya nemi ministan kwadago ya cire hannunsa a cikin sasantawar su da kungiyar malamai, cewar fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasar Najeriya ta karyata rahotannin dake bayyan cewa shugaba Buhari ya baiwa ministan Ilimi wasu makonni ya magance matsalar yajin aiki ASUU.

Hadimin shugaban kasa Garba Shehu ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter inda yace yawancin ‘yan jaridar kasar nan duk wallafa wannan labarin wanda bana gaskiya ba.

Yace Buhari ya gana da ministocin ne don magance matsalar yajin aikin kuma ministan ilimi ya ne ministan kwadago ya cire hannunsa a wanannan bantun domin ya samu damar kammala aikin nasa daya fara,

Karanta wannan  Gwamnatin Anambra tace babu wani dan takarar da zai saka fastocinsa a jihar face ya biya naira miliyan goma

Ministan Ilimin da kansa ya cewa shugaba Buhari da yardar Allah cikin makonni biyu zuwa uku zasu kammala sasantawa dasu.

Kuma ya kara da cewa idan har gwamnatin da kungiyar malaman suka bayar da hadin kai ma cikin kankanin lokaci za a magnace matslar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.