Kungiyar kwadago ta cigaba da gudanar da zanga zanga a fadin kasar Najeriya inda take nuna bacin ranta kan yajin aikin da kungiyar malamai ta ASUU keyi.
Kungiyar ta malaman jami’o’in Najeriya ta kasance tana yajin aiki tun a watan febrairu amma har yanzu gwamnati bata biya masu bukatunsu dalibai sun koma makaranta ba.
Wanda hakan yasa kungiyar kwadago ke taya su zanga zanga a fadin Najeriya, kuma shugaban kungiyar Ayuba da kansa tare da shugaban kungiyar malaman Emmanuel sun jagoranci zanga zangar a babban birnin tarayya Abuja izuwa majalissar dattawa.