fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Yajin aikin Kungiyar ASUU ya tilasta min farautar mijin aure cikin gaggawa – Wata dalibar ‘yar shekara 20 ta koka

Wata yarinya ‘yar shekara 20 da haihuwa kuma dalibar jami’ar jihar Gombe (GSU) mai suna Maryam Adamu, ta koka da yadda kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke ci gaba da yajin aiki wanda tilasta mata neman mijin aure cikin gaggawa.

Dalibar jami’ar GSU mai matakin karatu 200, ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da manema labarai a Gombe, inda ta ce yajin aikin ya ruguza shirinta da burinta kammala karatunta tun kafin ta kai shekara 20 da kuma burin yin aure bayan ta kammala karatunta.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Hukumar 'yan sanda ta kama shararren mawakin Najeriya Kizz Daniel a kasar Tanzania

Dalibar ta kara da cewa; ASUU da gwamnati za su iya ci gaba da wasansu domin kuwa a halin yanzu auren ne ke gabanta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.