Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa, yaki da ‘yan Bindiga akwai wahala.
Ya bayyana hakane ranar Asabar a wani gidan rediyo dake Legas.
Yace amma fa akwai laifin ‘yan Najeriya, dan kuwa basa bada hadin kai wajan fadar masu kai irin wadannan hare-haren.
Yace ya kamata mutane su rika taiamakawa jami’an tsaro da bayanai kan masu kai irin wadannan hare-haren ta yanda zasu iya magance matsalar.