fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Yakin Boko Haram ba akan addini bane>>Shugaba Buhari ya gayawa wakilan Kotun Duniya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyanawa wakilan kotun Duniya da suka ziyarceshi a fadar gwamnati cewa, yakin Boko Haram ba na addini bane.

 

Shugaban yace babu yanda za’a yi mutum ya kashe dan Adam sannan kuma ya rika fadin Allahu Akbar! Yace ko dai bai san Allahn ba ko kuma sakaraine.

 

Yace maganar kuma cewa Boko Haram ce yaudara ce, shiyasa Gwamnati ke yaki dasu kuma suna samun nasara sosai ana ilimantar da mutane.

 

Yace ya karbi mulki yayin da al’amura suka yi muni sosai amma yanzu suna ilmantar da mutane, kuma Ilimi na da muhimmanci.

Karanta wannan  Ana binciken ma'aikatar ruwa kan sayar da kadarar Biliyan 2 akan Miliyan 13

 

Shugaban yace wasu mutane kawai sun mayar da aikinsu shine kashe mutane da kawo rudani a cikin jama’a.

 

Wakilin kotun Duniya, Karin Khan ya yi kira ga Najeriya data rika kaiwa kotun Duniyar maganar ‘yan ta’adda dan yin bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.