‘Yan bindigar da sukayi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa na jihar Kaduna sun sake sako mutane biyar a yau ranar talata.
Cikin mutanen da suka sako hadda Mukhtar Shuaihu wanda suka harbe shi yayin da wasa da bindiga a cikin dajin a kwanakin baya.
Hadimin Sheik Ahmad Gumi, Malam Tukur Mamu ne ya bayyana hakan inda yace yanzu haka suna ofishinsa bayan ‘yan bindigar sun sako su.
Malam Tukur Mamu a kwanakin baya ya taka rawar gani wurin sako mutane 11 dake hannun ‘yan bindigar, amma daga bisani ya cire hannunsa a cikin wannan lamarin saboda tsaro.