A jiyane wasu ‘yan APC a kananan hukumomin Matazu da Musawa suka koma Jam’iyyar PDP.
Shugaban tawagar, Hon. Ali Maikano ya bayyana cewa, aun yanke shawarar canja jam’iyyar ne saboda yanda ake nuna musu rashin adalci a jam’iyyar APC.
Shugaban PDP na jihar, Hon. Salisu Yusuf Majigiri ya tabbatarwa da sabbin membobin nasu cewa, zasu samu adalci a jam’iyyar ta PDP.