fbpx
Saturday, May 28
Shadow

‘Yan APC sun koka da tsadar fom din takarar shugaban kasa na Miliyan 100, inda suka ce ko a kasar Amurka Miliyan 20 ake sayen Fom

Jam’iyyar APC dake da ofishi a kasar wace kudin fom din neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar ta APC yayi yawa.

 

Jam’iyyar APC tace Miliyan 100 ne zata sayar da fom din takarar ta na shugaban kasa inda kuma na gwamna za’a sayar akan Naira Miliyan 50.

 

Saidai ofishin kamfe din Phillip Idaewor dake kasar waje yace wannan kudi sun yi yawa sosai.

 

Yace ita kanta Amurka, kudin sayen fom din takarar shugaban kasar ta bai wuce $40,000 wanda kwatankwacin Naira Miliyan 20 ne.

Karanta wannan  Ka hakura da takarar shugaban kasa in ba haka ba zaka ji kunya>>Kungiyar Ohanaeze Indigbo ta gayawa Atiku Abubakar

 

Dan haka yace akwai bukatar jam’iyyar ta rage yawan kudin takarar fom din na shugaban kasa da ta sanya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.