fbpx
Thursday, February 25
Shadow

#StopKillingNortherners ‘Yan Arewa ciki hadda ‘yan Fim na kiraye-kirayen a daina kashe ‘yan Arewa a Kudu:Kalli Bidiyon yanda aka bankawa wasu Hausawa wuta da ransu

Matasan arewa sun fito a shafukan sada zumunta suna kira da a daina kashe mutanen Arewar a kudu.

 

Ana amfani da maudu’in #StopKillingNortherners ne wajan bayyana wannan rashin jin dadin.

 

Falalu A. Dorayi yayi kira ga hukumomi su dauki mataki akan lamarin inda yace yin kunnen uwarshegu dashi ba zai zama Avu me kyau ga kasarnan ba.

 

Hakanan Ali Nuhu, Sarki shima ya shiga wannan kiraye-kirayen na daina kashe ‘yan Arewa.

 

Me Amfani da sunan Waspapping a Twitter ya bayyana cewa, ya kamata Yarbawa su jawo hankalin mutanen su kan kisan da akewa Hausawa a Oyo, saboda hakan ba zai haifarwa kowa da mai ido ba.

 

 

Me Amfanibda sunan My deen my swag walafa wani hoton Bidiyo da ya nuna yanda aka bankawa wasu wuta, inda yace kalli yands ake kashe ‘yan Arewa.

 

 

Dan jarida, Mubarak Umar ya bayyana cewa zai ci gaba da watsa labaran dake dauke da wannan maudu’i har sai an ji koken da ake akan daina kashe ‘yan Arewa.

Shi kuwa wani me Amfani da Sunan Faarees ya wallafa wani Bidiyo ne inda aka ga tulin Hausawa na gudu. An ji wata murya a ciki na cewa kalli yanda Yarbawa ke korar Hausawa.

 

Ya koka da cewa kalli yanda Hausawa ke gudu dan tsira da rayuwarsu a a Ibadan jihar Oyo. A cikin kasarsu, yace rikici ba shine Mafita ba.

 

 

Shima dai Bulama Bukarti ya bayyana cewa kisan da akewa Hausawa a jihar Oyo ya kamata a dakatar dashi. Yace kuma ya kamata a kamo wanda suka aikata hakan dan hukuntasu.

 

Shima Sanata Shehu Sani yayi Allah wadai da kisan Hausawa a jihar ta Oyo, inda yace ya kamata gwamnatin jihar ta Kamo wanda suka aikata wannan abu ta hukuntasu.

 

Shima wani me sunan Engr Yasir Arafat Jubril ya wallafa hoton Bidiyo wanda ya nuna yanda akawa Kasuwar ta shasha dake Ibadan kurmus inda yace Allah kadai yasan adadin mutanen da aka kashe tsakanin Hausawa da yarbawa.

 

Yayi zargin cewa jami’an tsaro na wajan amma sun ki harbi da cewa wai ba’a basu Umarni ba.

 

Gimba Kakanda yace a shekarar 1993 da tsohon shugaban kasa, IBB ya soke zaben Yuni 12, Hausawa suka dandana kudarsu. Amma an manta da yanda Hausawan suka ki zabar dan takararsu, Bashir Tofa suka zabi Abiola. Yace hakanan a shekarar 1998 da Abiola ya mutu, an zargi Hausawa inda a nan ma aka kashesu, yace dole a dakatar da wannan haukan.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *