An kashe shugaban ‘yan bindigan da suka kai hari Takakume a jihar Sokoto jiya ranar lahadi.
Yan bindigar sun kai harin ne cikin dare inda suka kashe mutun guda kuma suka yi garkuwa da wasu guda shida.
Amma ‘yan banga sunyi nasar bude masu wuta inda kashe masu shugabansu, wanda daga bisani aka gano cewa shima ya taba zama a garin na Takakume.