‘Yan bindiga sun kona kasuwar Izombe dake karamar hukumar Aguta yau ranar litinin a jihar Imo.
Sun kona kasuwar ne saboda ‘yan garin sun saba dokar da suka sa masu ta zama a gida dole a kowace ranar litinin.
Inda suka kona kasuwar suka jiwa masu shaguna rauni tare da kona wasu motoci a kasuwar.