fbpx
Sunday, August 7
Shadow

‘Yan bindiga na can sun budewa mutanen da sukayi garkuwa dasu a jirgin kasan Kaduna wuta

‘Yan bindigar da sukayi garkuwa da mutane a jirgin kasa na jihar Kaduna zuwa Abuja sun harbi daya daga cikin fasinjojin, Muhammad Al’amin.

‘Yan bindigar sun harbe shi ne yayin da suke wasan harbe-harbe a cikin jejin da suke tsaronsu domin su basu tsoro kar wani yayi yunkurin tserewa.

Malam Muhammad Mamu ne ya bayyana hakan a yau ranar laraba, wanda ya gana da ‘yan bindigar suka sako mutane 11 a baya.

Kuma yace idan har gwamnatin tarayya na son mutanen su dawo da ransu to ya kamata ta gaggauta daukar mataki akan  wannan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.