fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

‘Yan bindiga sun ƙi sakin dagacin Rijana da ‘ya’yansa ‘duk da biya musu buƙatunsu’

Yan bindigar da suka sace dagacin garin Rijana na Jihar Kaduna har yanzu na ci gaba da riƙe shi da ‘ya’yansa duk da cewa an biya musu wasu buƙatu da suka nema.

‘Yan fashi masu garkuwa da mutane sun sace Dagaci Ayuba Dodo Dakolo ranar Alhamis tare da ‘ya’yan nasa uku a gonarsa da ke yankin.

Sai dai wani mazaunin yankin da ke da ilimin yadda lamarin ya faru ya shaida wa BBC Hausa cewa sun sako biyu daga cikin ‘ya’yan nasa. Amma ya nemi mu ɓoye sunansa.

Sai dai kuma baya ga ‘ya’yan nasa, ‘yan bindigar sun sace wasu ‘yan mata da samari fiye da 10 waɗanda su ma ke hannunsu ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Garin Rijana na kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, wadda ta yi ƙaurin suna wajen sace-sacen mutane da ‘yan fashin daji ke yi.

Bayan an biya musu buƙatun da suka nema sai suka turo da wasu’

“Jiya (Alhamis) sun ce suna buƙatar a saya musu man fetur da shinkafa da sauran wasu abubuwa kuma a kai musu, kuma na samu labarin an yi duka waɗannan abubuwa amma suka ƙi sakin sa,” a cewar majiyar.

Mutumin ya ƙara da cewa bayan an kai musu kuma sai suka sake gindaya wasu sharuɗɗan.

Halin da ake ciki a Rijana

Garin na Rijana na cikin halin jimami, inda mutane suka yi cirko-cirko suna jiran tsammani, in ji mutumin.

“Lokacin da na je ban tarar da jami’an tsaro a gidan sarkin ba, amma dai akawai talakawansa da mukansantansa suna jiran su ji ci gaban da aka samu daga wajen ‘yan bindigar.

“Tabbas akwai jami’an tsaro, suna nan a bakain titi. Kana zuwa za ka gan su suna kaiwa da komowa. Amma matsalar ita ce, yanzu sun (‘yan bindigan) ce ba za su bari a yi noma ba.

“Ko a jiya an gan su kan babura da yawa sun yi gabas, sun sake nausawa cikin dajin.

“A cikin gari, jami’an tsaro na ba mu haɗin kai gaskiya. Akwai DPO a garin, da kuma kaftin ɗin soja da ke kula da rundunar soja da ke kula da sintiri a kan hanya. Sai dai ko suna da wani shiri mu farar hula ba za mu sani ba.”

Mutumin ya ƙara da cewa manoma na cikin fargaba “saboda idan har mutum ya bar garin da kilomita ɗaya ba lallai ne ya dawo ba”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.