‘Yan bindiga sun kashe mutane takwas a taron bikin suna da akayi a wani kauye na Sandiaba dake Burkina Faso.
Wannan lamarin ya faru ne a ranar litinin 28 ga watan mayu a cewar manema labarai na AIB, inda ‘yan bindigar suka afka cikin taron suka bude maau wuta.
Inda suka ce kasar na fama da matsakar tsaro sosai duk da kokarin da jami’anta keyi na samar da tsaro a kasar.