‘Yan Bindiga a jihar Filato sun baiwa wasu kauyuka 5 gargadin cewa su tashi daga kauyukan nasu ko kuma su kai musu hari.
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sanine ya bayyana haka a shafinsa na sada zumunta.
Sanata Sani yace ya kamata jami’an tsaro su kaiwa wadannan kauyuka dauki saboda ‘yan Bindigar yawanci idan suka ce zasu yi abu basa fasawa.