fbpx
Friday, July 1
Shadow

Yan bindiga sun bude wuta a Philadelphia dake kasar Amurka sun kashe mutane uku sun jiwa 11 rauni

Yan bindiga sun harbi mutane 14, uku sun mutu a Philadelphia dake kasar Amurka ranar asabar da dare.

Lamarin ya faru ne a kudancin Philadelphia inda hukumar ‘yan sandan suka bayyana cewa sun ji karan harbin bindiga da kuma ihun mutane.

Inspecta Pace ya kara da cewa wani jami’i ya harbi daya daga cikin ‘yan bindigar wanda hakan yasa suna jefar da bindigunsu suka tsere.

Gabadaya mutanen da suka harba duk an kaisu asibiti wanda a can ne maza biyu da mace daya suka rasa rayukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.