fbpx
Monday, August 3
Shadow

‘Yan bindiga sun bukaci a biyasu fansar Miliyan N16 su saki matar da suka sace a jihar Ribas

Wata mata wadda aka bayyana da suna  Nyieda Kpeenu mai kimanin shekaru 60 dake garin Nweol a karamar hukumar Gogana jihar Ribas, ta shiga hannun wasu ‘yan bindiga ne a ranar laraba, inda ‘yan bindigar suka nemi fansar kudin har kimanin Naira miliyan 16 domin sakinta.

Wata majiya ta kusa ta bayyana cewa ‘yan bindigar sunyi nasarar sace Kpeenu a ranar laraba da misalin karfe 8 na dare, inda sukai ta harbi a sama domin tsoratar da mazauna yankin.

Wani dan wanada lamarin ya rutsa da shi, ya shaidawa jaridar vanguard cewa ‘yan bindigar sun sace mahaifiyarsu, haka zalika bayan kwana biyu sun kirasu da su biya fansar kudi kimanin Naira miliyan 16 don sakinta.

“Ina zamu samu kudi kamar haka, mahaifiyarmu ba ‘yar siyasa bace, ita manomiya ce, mun kai rahoto ga ‘yan sanda amma babu matakin da a ka dauka, dan haka zamuyi ta’addu’a domin wadanda suka saci mahaifiyarmu suji tausayin mu su sake ta batare da wata fansa ba.Injishi

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, a jihar Ribas, SP Nnamdi Omoni, ya ce ba a kai karar ofishin nasa ba, ya yi alƙawarin zai tuntuɓi ofishin ‘Yan sanda da ke kula da yankin don tabbatarwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *