‘Yan bindiga sunyi garkuwa da wata mata tare da jinjirinta dan wata hudu a duniya da kuma mijinta da dan aikensu a kauyen Rafin Ciyawa dake karamar hukumar Ningi.
Wannan lamarin ya faru ne a daren ranar alhamis wato ranar 28 ga watan Yuli da misalin karfe biyu na dare a jihar Bauchi.
Yayin da shugaban karamar hukumar ta Ningi, Mamuda Hasan ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun sako matar tare da jinkirin nata bayan an biya su wasu kudade.
Amma sun cigaba da rike mijinta nata wanda ya kasance dan kasuwa tare da dayan yaron, kuma sun bukaci naira miliyan goma kafin su sako su.