Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe dan majalisar mai wakiltar mazabar Aguata II a majalisar dokokin jihar, Hon Okechukwu Okoye.
An yi garkuwa da dan majalisar a makon da ya gabata, tare da wani mutum daya a cikin motarsa Toyota Sienna da wasu mutane da ba a san ko su waye ba.
A ranar Asabar, 21 ga watan Mayu, an gano kan sa a Nnobi, cikin karamar hukumar Idemili ta kudu a jihar Anambra, inda aka rataye shi yayin da masu kisan suka ajiye sauran gangar jikinsa.
Karanta wannan An yiwa mata fyade tare da 'yarta a motar da suka hau don a rage masu hanya zuwa gida
Da take tabbatar da wannan ci gaban, gwamnatin jihar a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta yi Allah wadai da lamarin tare da bayar da tukuicin Naira miliyan 10 ga duk wanda ya bada bayanai masu amfani da za su kai ga kama wadanda suka aikata laifin nan take.