fbpx
Friday, August 12
Shadow

‘Yan bindiga sun kai hari bankin UBA sun kashe mutun guda a jihar Abia

‘Yan bindiga sun kai hari Bankin UBA dake Umahia a jihar Abia yau ranar alhamis kuma sun kashe mutun guda.

Sai dai babu tabbancin mutumin da suka kashe ko ma’aikacin bankin ne ko kuma abokin cinikinsu.

Amma mazaunin yankin da wannan lamarin ya faru a gabansa, Kingsley ya bayyana cewa mutumin kayan marmari yake sayarwa.

Kuma bayan sun harbe an gaggauta kai shi asibiti wanda a can ne wa’adinsa ya cika, kuma hukumar ‘yan sndan jihar sun ce ba sata ‘ya  bindigar suka je yi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.