fbpx
Sunday, March 26
Shadow

‘Yan bindiga sun kai hari jihar Katsina sun kashe mutane uku yayin da kuma sukayi garkuwa da wasu mutane marasa adadi

‘Yan bindiga sun kai hari jihar Katsina a kauyen Dantsauni dake karamar hukumar Batagarawa, inda suka kashe mutane uku sukayi garkuwa da wasu mutne masu yawa.

Wani mazaunin kauyen ya bayyanawa manema labarai na Channels cewa ‘yan bindigar sun kai wannan harin ne da musalin karfe 3:55 na yamma a ranar laraba.

Inda yace sun mamaye kauyen ne yayin da mutane ke kokarin yin Sallar La’asar kuma sunta harbe-harbe har suka kashe mutane uku kafin sukayi garkuwa da wasu mutane.

Kuma yawancin wa’yanda sukayi garkuwa dasu mata ne da yara domin sauran mutanen sun tsere, yayin da kuma mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda na jihar, Gambo Isa ya tabbatar da wannan harin.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *