Fasinjoji da dama sun bata bayan da ‘yan bindiga suka kaiwa jirgin ruwa hari a jihar Cross Rivers.
Wata mata ce cikin fasinjonin jirgin ta wallafa bideyo ta nemi agaji wurin hukuma bayan ‘yan bindigar sun kai masu harin a Calabar.
Domin tace ‘yan bindigar sun sace masu ganadaya kayayyakinsu kuma sunyi garkuwa da gabadaya mazajen dake cikin jirin hadda direba.
Su kuma mata ne basu iya tuka jirgin ruwa ba saboda haka ne ta nemi agaji kuma hukuma ta kawo masu dauki.