fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Yan bindiga sun kai hari kan ƙauyukan Katsina, inda suka kashe mutum 3

‘Yan bindiga a daren ranar Alhamis sun kai hari kan kauyukan Madobai da Dannakwabo na karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu da yawa.

 Mazauna garin sun ce da yawa daga cikin dabbobinsu da kayan abinci su ‘yan fashi suka kwashe bayan mamayar.
 
A Cesar wata majiya mazauna yankin sun binne gawarwakin da safiya bayan sun musu sallar jana’iza haka zalika majiyar ta bayyana yadda mazauna yankin suka koka bisa yawan harin da ake kaiwa yankin nasu. Hakan ya zo ne kwana guda bayan da aka kai hari kauyen Mabai a cikin gunduma guda daya, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wani manomi, Sada Musa, yayin da wani Karibu Mohamed aka harba da harsashi.
 
 
Mazauna kauyen sun yi ƙoƙari su tare harin amma a sakamakon yawan da ‘yan bindigar ke dashi wanda suka haura 70 akan baburaran su, ya sanya suka kasa cimmusu.
 
 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  An kama matar data sace diyar makwabtanta

Leave a Reply

Your email address will not be published.