Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun far wa al’ummar ne da sanyin safiyar yau Juma’a, inda suka shafe sa’o’i da dama.
An yi garkuwa da mutane da dama daga kauyen Danjanku da ke karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a yankin, kamar yadda siyasar Najeriya ta bayyana.
Rahoton ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun yi kaurin suna wajen kai farmaki ga al’umma da sanyin safiyar yau Juma’a, inda suka shafe sa’o’i da dama.
‘Yan ta’addan sun isa kauyen ne a kan babura kafin su yi harbi ba kakkautawa. Sun yi awon gaba da wasu mutanen yankin inda suka tsere da su cikin dajin.
Allah ya saukake.