fbpx
Monday, June 27
Shadow

Yan bindiga sun kai hari kauyen Katsina, sun bindige wasu manoma 15

Wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla manoma 15 a kauyen Gakurdi da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

An tattaro cewa an kashe wadanda aka kashe ne a safiyar Talata, 24 ga watan Mayu, yayin da suke gyara gonakinsu a wajen kauyen gabanin damina.

Wani mazaunin garin ya shaida wa Aminiya cewa ‘yan bindigar da suka hau kan babura hudu, tun farko sun nufi kauyen Gakurdi ne amma da suka ga manoman sai suka fara harbi.

Yace a lokacin da mutanen kauyen suka gano abin da ke faruwa, maharan sun gudu daga yankin.

Karanta wannan  An damke mutumin daya kashe wata mata mai yara biyu a jihar Anambra

Shima da yake magana, wani mazaunin unguwar Daddara, Bashir Salihu, ya ce ‘yan bindigar sun kuma kona wasu gidaje.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Gambo Isa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wasu ‘yan bindiga 8 a kan babura hudu ne suka kai harin.

Kakakin ya kara da cewa wasu mazauna garin suna da bindigu amma wani yaro ne kawai ya tsaya tsayin daka ya harbe ‘yan bindigar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.